10 Maris 2020 - 10:34
Sojojin Amurka Sun Fara Janyewa Daga Kasar Afghanistan

A jiya Litinin ne dai sojojin na Amurka da su ke a kasar Afghanistan su ka sanar da fara janyewa daga kasar Afghanistan domin aiwatar da yarjejeniyar Doha da su ka cimmawa da kungiyar Taliban.

(ABNA24.com) A karkashin waccan yarjejeniyar dai Amurkan za ta rage yawan sojojinta da su ka kai 8,600 daga Afghanistan a cikin kwanaki 135.

Kakakin sojan Amurka kanar Sonny Leggettya fada a cikin wani bayani cewa; Za mu bar sojojin da ake da bukatuwa da su domin kai farmaki akan mayakan Isis da kuma karfafa sojojin Afghanistan.

Yarjejeniyar ta kunshi cewa a karkashin kwanaki 10 ne daga rattaba hannu a fara janye sojojin.

A gefe daya kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambaci cewa; Amurka tana son kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya kada kuri’ar amincewa da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar Taliban.

Wannan matakin na fara janyewar sojojin Amurka ya zo ne dai a daidai lokaci aka kafa gwamnatoci biyu masu cin karo da juna a kasar ta Afghanistan.

Shugaban kasa mai ci, Ashraf Gani da kuma abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah, kowanensu ya saba layar rantsuwa a matsayin halartaccen shugaban kasa.

Zaben shugaban kasar da aka yi a cikin watan Satumba ya nuna cewa Ashraf Ghani ya sami nasara da rinjaye mafi karanci, lamarin da Abdallah Abdallah ya musanta yana mai bayyana kansa a matsayin zababben shugaban kasa.



/129